Rashin tsaro na kara yawa a Burkina Faso
February 17, 2020'Yan bindigar dai sun kai harin ne a wani Cocin Protestant da ke wani kauye a yankin Arewacin kasar. Haka kuma wata majiyar tsaro ta tabbatar da cewa sojojin kasar biyar sun halaka sakamakon bam da aka dana a kan hanya, a yankin da ke fama da tashe-tashen hankula. Gwamnan Lardin Kanal Salfo Kabore ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faranasa na AF cewa, gungun 'yan bindigar dauke da makamai sun kai harin ne a kauyen Pansi da ke Lardin Yagha inda suka halaka mazauna yankin bayan sun ware baki daga cikinsu. Tun dai daga shekara ta 2015 kawo yanzu, mutane 750 ne aka tabbatar sun halaka yayin da wasua kimanin dubu 600 suka tsere daga gidajensu a Burkina Fason, da ke zaman guda daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya da ke kuma fama da matsalar 'yan ta'adda masu tayar da zaune tsaye a yankin Sahel.