Sabon kawance tsakanin Burkina Faso da Mali
February 2, 2023Talla
Tayin na zuwa ne a daidai lokacin da kashashen biyu suka raba gari da Faransa bayan korar dakarunta dake jibge a Mali da Burkina Faso.
Firaiministan na Burkina Faso Apollinaire Kyélem de Tambela ya mika wannan bukata ce yayin da ya kai ziyarar kwanaki biyu a kasar Mali inda ya ce kasashen biyu na iya hada karfinsu guri daya cikin mutumta dokokin ko wace kasa don dawo da tsaro a yankinsu.
Ko baya ga harkar tsaro Firaiministan na Burkina Faso na kyautata fatan ganin kasarsa da Mali sun kula hulda mai karfi a fannin bunkasa albarkatun karkashin kasa da noma da kiwo da Allah ya huwace masu, abin da a fadar sa zai taikawa wa kasashen biyu da ake gani tamkar saniyar ware wajen dogaro da kansu ta ku dakile talauci.