Burkina Faso ta mamaye jaridun Jamus
November 15, 2019Za mu dauko sharhin jaridun na wannan lokaci da Berliner Zeitung wadda ta leka taron Majalisar Dinkin Duniya bisa kyautata zaman iyali tana mai cewa yawan karuwar mutane a duniya ya ragu amma ban da yankin Kudu da Sahara na Afirka sakamakon karancin ilimi ga yara mata gami da rashin samar da wadatattun magungunan tazara na haihuwa.
Duk da haka Gimbiyar kasar Denmark mai jiran gado Mary ta yaba da taron farko na Majalisar Dinkin Duniya makamancin wannan shekaru 25 da suka gabata a birnin Alkahira na kasar Masar da ya duba tsarin iyali, kuma yanzu aka sake gudanar da wani wanda ya kawo karshe a wannan Alhamis da ta gabata a birnin Nairobi na aksar Kenya. Fiye da wakilai 6,000 daga sassa daban-dabam na duniya suka halarci taron. An amince cewa tsarin zai kyautata idan aka samar da ci-gaban tattalin arziki gami da tazara tsakanin haihuwa, kuma mata suna da muhimmiyar rawar da za su taka.
Kasuwar Intanet a Afirka ya ja hankalin jaridun Jamus Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta bude da taken fadada kasuwar zamani ta hanyar intanet a Najeriya, inda jaridar ta ce watanni bakwai bayan gagarumar nasarar da kafar Jumia mai sayar kaya ta kafar intanet ta samu a Najeriya, yanzu kuma an sake samun Interswitch daga birnin Lagos na Najeriya wanda ya dauki hankali a nahiyar Afirka. A cewar kamfanin ya yi cikayayya na fiye da milyan 500 ne Euro cikin jadawalin aikace-aikace wata-wata da ya fitar.
Dabbobi na da matsalar matsaguni a Zimbabuwe Har ila yau jaridar ta Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce gagarumin samar da matsaguni ga dabbobi a tarihin Zimbabuwe, inda ta ce bayan mutuwar kimanin giwaye 120 sakamakon kishin ruwa a gungudajin kasar, yanzu haka mahukunta a birnin Harare sun dauki gagarumin matakin tsugunar da kimanin giwaye 600 gami da wasu daruruwan dabbobi kamar yadda hukumar kula da gundun daji ta kasar ta bayyana. Matakin na fara aiki cikin tsakiyar wannan wata na Nowamba.
Tsokacin jaridun Jamus kan matsalolin tsaro a Burkina Faso Ita kuwa jaridar der Freitag ta mayar da hankali kan kasar Burkina Faso a sharhi mai taken kasar ta lamura suke sukurkucewa inda ta ce kasar da ke yankin yammacin Afirka tana karkashin hare-haren masu Jihadi da kabilanci. Jaridar ta kara da cewa gwamnati ta rasa iko da akasarin yankunan arewa da gabashin kasar. Akwai kimanin mutane rabin milyan da suka rasa matsugunansu rabi daga ciki a watanni uku da suka gabata. Akwai yara kimanin 300,000 da ba sa zuwa makarantu sakamakon hare-hare masu Jihadi a makarantu da cibiyoyin koyarwa. Yanzu haka akwai 'yan kasar ta Burkina Faso fiye da milyan daya da rabi wadanda suka dogara kan agajin jinkai.
Matsalolin da Burkina Faso ta samu kanta a ciki suna nasaba da abin da ke faruwa a makwabciyar kasar ta Mali, wadda masu Jihadi suka mamaye a shekara ta 2012. Sojojin Faransa suka taimaka wa sojojin Mali aka fatattaki masu Jihadin kuma wasu daga cikin sun kutsa Burkina Faso, wadda a 'yan watannin da suka gabata kungiyar kula da 'yan hijira ta duiniya take dauka a matsayin mai kwanciyar hankali tare da tunanin mayar da wasu daga cikin bakin haure Libiya zuwa kasar ta Burkina Faso kafin lamura su cakude mata.