Burkina Faso ta sake dakatar da wasu kafafen yada labarai
April 29, 2024Burkina Faso ta sake dakatar da wasu kafafen yada labarai daga yada shirye-shiryensu a kasar, sakamakon fitar da rahoton hukumar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch, da ta zargi sojojin kasar da yi wa wasu mutanen karkara fararen hula 223 kisan gilla.
Karin bayani:Burkina Faso ta yi fatali da zarge-zargen Human Rights Watch
Kafafen yada labaran da dakatarwar ta yanzu ta shafa sun hada da Deutsche Welle da ke nan Jamus, da jaridar Faransa ta Le Monde, da Quest-France, sai jaridar Guardian ta Burtaniya da kamfanonin dillancin Afirka na APA da kuma Ecofin.
Karin bayani:Burkina Faso ta dakatar da shirye-shiryen BBC da VOA
Tun da farko dai Burkina ta fara dakatar da BBC da VOA, da kuma gidan talabijin din Faransa na TV5Monde.
Karin bayani:Ana zargin sojojin Burkina Faso da kashe fararen hula 223
Rahoton na Human Rights Watch ya zargi sojojin Burkina Faso da hallaka fafaren hular 223 a cikin watan Fabarairun da ya gabata, bisa zarginsu da hada baki da 'yan ta'adda.