Burkina Faso za ta dauki sabbin dakarun soji
February 24, 2023Talla
A cikin sanarwar da ministan tsaron kasar kanal Kassoum Coulibaly ya fitar, ya ce za a dauki sabbin dakarun da ba su aiki a yanzu ne daga sassa daban-daban na kasar. Ya kara da cewa za a ci-gaba da daukar matasan sojojin ne daga ranar 28 ga watan Fabarairun zuwa 7 ga watan Maris din wannan shekarar, wadanda aka haife su tsakanin shekarar 1988 zuwa shekarar 2003.
Wannan dai shi ne karo na uku cikin tsukin shekara guda da rundunar sojin ta dauki sabbin jami'ai. Kasar Burkina Faso ta shafe shekaru ta na fama da matsalar tsaro wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dubu 1 yayin da wasu miliyan 2 suka rasa matsugunansu.