An dakatar da mujallar Jeune Afrique a Burkina
September 26, 2023Talla
Hakan kuwa ya biyo bayan wani labarin da jaridar ta buga cewar akwai rikici da rishin zutuwa a tsakanin sojojin kasar da suka fara tayar da bore a cikin barakokin sojin. A cewar gwamnatin Burkina Fason wadannan maganganun da aka yi da gangan ba tare da wata hujja ba, na da burin zubar da mutuci da kuma martabar sojojin kasar abinda ta ce ba za ta amince da shi ba. Mujallar ta Jeune Afrique wacce aka kirkiro a shekara ta 1960, wata kafar watsa labarai ce, ta Afirka da Faransa wacce ke da hedkwata a Faransar, kuma tana da wakilai da yawa a Afirka da sauran yankuna.Tun farkon gwamnatin ta Burkina Faso ta dakatar da tashar gidan rediyion RFI da talabijan na France 24 saboda abinda ta kira bayyana labaran karda kazon kurege.