1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Bankin CBN ya yi fatali da 'yan Arewa

February 12, 2021

A daidai lokacin da ake ci gaba da fama da talauci da rashin tsaro a arewacin Najeriya, kungiyar dattawan yankin ta zargi babban bankin CBN da nuna wa Arewa wariya wajen tafiyar da harkokin kudi.

https://p.dw.com/p/3pIH4
Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Babu banki ko daya daga cikin manyan bankunan Najeriya 25 dake zama mallakin mutanen arewacin Najeriya, haka kuma bankuna 200 ne a cikin dari tara na kananan ke zaman mallakar sashen da ke da yawan al'umma kuma na kan gaba ga batun fatara da talauci, lamarin da ya tada hankalin dattawan arewacin kasar dake kallon da biyu a harkokin babban bankin CBN ga yankin na Arewa.

Karin Bayani: Hanyoyin fita daga matsalar kudi a Najeriya

Cikin wata wasikar da ta aikewa bankin, kungiyar dattawan arewacin Najeriya ACF, ta ce akwai alamu na wariya ga yadda bankin ke bayar da tallafin kudi ga yankin kudancin kasar, yana mantawa al'ummomin Najeriya mazuna yankin arewacin kasar. Wani umarnin babban bankin na sake habbaka hannun jarin a Arewa, na zama babban sanadin rikici, a cewar Malam Murtala Aliyu sakataren kungiyar dattawan a tattaunawar da yayi da tashar DW. 

Karin Bayani: Kalubalen kudin Cryptocurrency

Nigeria Geldwechsler
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Duk da cewar sashen arewacin Najeriyar ya dade yana taka rawa wajen tabbatar da shugabancin siyasa a kasar, ana kuma ganin sashen ya dauki lokaci  yana zaman na kurar baya ga batun tattalin arzikin kasar. Rashin bankunan a sashen arewacin kasar dai na da ruwa da tsaki wajen karuwar talaucin da wasu jihohin yankin ke fama da shi, wanda kuma masana ke ganin cewa kaso 80 cikin dari na daukacin al'ummar yankin Arewa na fama da kuncin rayuwa da fatara da talauci. Malam Yusha'u Aliyu dake zaman masani tattali arziki a Najeriya, ya ce "Rashin harkokin kudi tsakanin al'umma na zaman ummul'aba'isin rashin tsaron dake kara ta'azzara tsakanin al'umma a arewacin Najeriya." 

Karin Bayani: Sabon kasafin kudi don cigaban tattalin arzikin Najeriya

Wata kiddigar da bankin duniya ya fitar ya nuna cewa kaso 87 cikin dari na matalutan Najeriyar na sashen arewacin kasar, duk da yake yana kunshe da kaso 60 cikin dari na daukacin al'ummar Najeriya.