1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cece kuce a kan ɗaukar matakin soji a Siriya

August 26, 2013

Tawagar masu binciken makamai na Majalisar Ɗinkin Duniya ta fuskanci hare-hare a hanyar zuwa yankunan da a ke zargi yin amfani da makamai masu guba a yaƙin Siriya.

https://p.dw.com/p/19WCv
epa03837850 The convoy of UN inspectors is seen leaving the Four Seasons hotel in Damascus, Syria, 26 August 2013. UN weapons experts set out from Damascus to Eastern Ghouta, the area on the outskirts of the Syrian capital, where chemical weapons were allegedly used and over which West has warned of consequences for the regime of President Bashar al-Assad. The opposition said the 21 August bombardment by government forces using a poisonous gas left 1,300 people dead. The government has vehemently denied the claim. EPA/STR +++(c) dpa - Bildfunk+++ ***FREI FÜR SOCIAL MEDIA***
Hoto: picture-alliance/dpa

Manyan jami'an soji daga ƙasashen da suka haɗa da Faransa, Jamus, Birtaniya, Italiya da Kanada. Sai kuma Saudiya da Turkiya da kuma daular Qatar ne ke hallara a ƙasar Jordan domin tattauna irin tasirin da yaƙin basasar Siriya ke da shi ga yankin.

Kamfanin dillancin labaran Jordan, ya ce babban hafsan tsaron ƙasar, Meshaal Mohamed -Al-Zaban, tare da hadin gwiwar janar Lloyd Austin, kwamandan rundunar Amirka da ke kula da kasashe 20 a yankin Gabas Ta Tsakiya da kuma nahiyar Asiya ne suka kira taron na kwanaki biyu, wanda ke zuwa a dai dai lokacin da sakataren tsaron Amirka Chuck Hagel, ya sanar da cewar, faDar shugaban Amirka ta White House, ta shirya tsaf domin tinkarar duk wata matsalar da ka iya tasowa, wadda ta shafi batun yin anfani da makamai masu guba a yakin basasar Siriya:

Ya ce "Shugaba Obama ya buƙaci ma'aikatar tsaron Amirka, da ta tsara shirye-shiryen ko ta kwana, kuma tuni muka yi hakan. Kazalika, a shirye muke mu aiwatar da kowanne daga cikin zabin da ke gabanmu, idan ya yanke shawarar yin hakan."

British Foreign Minister William Hague speaks at an Australian-British Chamber of Commerce lunch in Sydney, Wednesday, Jan. 19, 2011. Hague is visiting Australia for the Australia-United Kingdom Ministerial Consultations. (AP Photo/Rick Rycroft)
William Hague, ministan wajen BirtaniyaHoto: AP

Daukar matakin soji a kan Siriya

Sai dai a hirar da wata jaridar Rasha ta yi da shugaban Siriya Bashar al-Assad, ya yi wa Amirka kashedin cewar, rashin nasara na tare da ita, idan har ta kuskura ta afkawa Siriya da yaki, kamar yadda ita ma gwamnatin Rasha ta yi wa gwamnatin kasar ta Amirka kashedi game da hatsari da kuma kuskuren da ke tattare da daukar matakin soji a Siriya, amma kuma ministan harkokin wajen Birtaniya William Hague, cewa yayi matsayin gwamnatin Birtaniya a fili yake dangane da matsalar yin amfani da makamai masu guba a yakin Siriya, kuma za su yi gaban kansu ko da ba tare da izinin Majalisar Dinkin Duniya ba:

Ya ce "Mu, a cikin gwamnatin Birtaniya mun bayyana a fili cewar, gwamnatin shugaba Assad ce ta kaddamar da hari da makamai masu guba, waɗanda suka yi ta'addi mai yawa. Dukkan hujjojin da a ke dasu a hannu suna nuni da hakan. Kama daga shaidun gani da ido, har ya zuwa ga kasancewar dakarun gwamnatin ne ke kaddamar da hare hare a yankunan, yayin da a ka kai hari da makamai masu gubar."

FILE- in this Oct. 11, 2012 file picture, France's Foreign Minister Laurent Fabius speaks at a press conference at French Foreign Ministry in Paris. Fabius told Europe-1 radio Sunday, Oct. 21, 2012, it's likely that Syrian President Bashar Assad's government had a hand in the assassination of Lebanon's intelligence chief Brig. Gen. Wissam Al-Hassan in a Beirut bombing. Fabius told that while it wasn't fully clear who was behind the attack that killed al-Hassan and seven others, it was "probable" that Syria played a role in the blast. (Foto:Francois Mori, File/AP/dapd)
Laurent Fabius, ministan wajen FaransaHoto: AP

Sakamakon binciken zargin anfani da makamai masu guba

Can a Faransa ma, gwamnatin ƙasar, ta bi sahun ƙasashen Amirka da Birtaniya ne wajen bayyana matsayinsu a kan batun yin anfani da makamai masu guba a kasar ta Siriya. Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius, ya ce babu abin da suke jira illa kammala tantance sahihancin labarin domin yin abin da ya dace:

"Da zaran an tabbatar da wannan zargin, hakan zai bamu kwarin gwiwa na mayar da martani. Sai dai kuma ku yi mini uzuri domin ba zan fadi irin matakin da zamu dauka ba a yanzu."

Kasar China wadda ke ɗasawa da Siriya kuwa, bayyana buƙatar nuna goyon baya ga tawagar binciken Majalisar Dinkin Duniya a kan batun makamai masu gubar ta yi, tana mai yin kira ga nuna halin dattaku game da duk wani martanin da kasashen duniya za su dauka a kasar, kana da rungumar tafarkin siyasa wajen warware rikicin kasar, maimakon ƙarfin soji.

Daga ƙasa za a iyasauraron wannan rahoto haɗe da martanin sauran ƙasahe

Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita: Abdourrahman Hassane

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Nuna karin labarai