1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cece-kuce kan kudin man fetir da suka yi batar dabo a Najeriya

July 11, 2014

Furucin 'yan majalisar dattawan Najeriya na cewa babu kudin man da ya bata ya janyo cece-kuce sosai daga al'ummomin kasar da ma masu fafutukar yaki da cin hanci da rashawa

https://p.dw.com/p/1CbVq
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

A Najeriya tabbatarwar da majalisar dattawan kasar ta yi kan cewar babu ko sisin kwabo da aka sace a kudin man fetir din nan na dalla bilyan 49 da suka haifar da cece kuce a tsakanin gwamnati da tsohon gwamnan babban bankin kasar ya haifar da maida martani daga masu fafutukar yaki da cin hanci da rashawa. Daga Abuja Uwaisu Abubakar ya aiko da wannan rahoton.

Kwamitin dattawan Najeriyan da ya gabatar da rahotonsa a kan zargin batan dabo da kudadden man suka yi har dalla bilyan 49, da majalisar ta yi mahawara tare da wanke duk wani zargin da aka yi na sace kudadden man fetir din ne ya samar da sabon babi a badakalar da ta kaiga dakatar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya watau mai martaba sakin Kano Sanusi Lamido Sanusi wanda ya bankado wannan batu.

To sai dai tabbacin da majalisar dattawan Najeriyar ta bayar cewa akwai kudadden da ba'a sanya a asusun gwamnatin Najeriyar ba da suka kai Dalla milyan 447 da kuma makuddan kudadden da kamfanin mai na NNPC ya kashe ba tare da izini ba ya sanya Barrsiter Mainasara Umar Faskarai da ke sharhi a kanb al'mmuran yau da kullum bayyana cewa akwai tufka da warwara a al'mari don me ya raba kin sanya kudadden da kuma sace su.

‘'To wannan abin dariya ne domin su kasnu sun amince cewa wannnan kudi da suke Magana maimakon su fito su ce sun bace ko an sace sai suka tabbatar dab au kudin danan, amma sai suka ce aa an dai yi amafani da kudin ne ba tare da izini ba, to ai duk wani abinda ba'a yi kasafin kudi ba aka kashe shi koda sisin kwabo ne to haramun ne ga tsarin aiki na gwamnati''.

Duk da hakikancewar da majalisar ta yi a rahoton da Sanata Ahmed Makarfi ya gabatar a kan babu kwabon da ya salwanta na man lamarin na zama abin mammaki ga mafdi yawan ‘yan Najeriya da suka dade da sa idon gano inda aka nufa da kudadden. Sanata Solomon Ewuga ya bayyana abinda ya sa suka gamsu da cewa babu sisin kwabo da wuya ya bace.

Goodluck Jonathan Präsident Nigeria ARCHIV 2013
Kamfanin mai na NNPC ya kashe makudan kudi ba tare da izini baHoto: picture-alliance/AP Photo

‘'Yace na farko yawan kudin ba Kaman yadda an bayyana bad a farko an ce dalloa bilyan 49, said a an je wajen bincike shi wanda ya bankado lamarin mai martaba sakin Kano sai yace yana ganin lissafi ya ragu tsakanin dalla bilyan 10 zuwa 20. Da kuma an bi ana bincike sai yace ai bai ce kudin sun bata bane, amma asusun gwamnati basu karba bane. To ai kaga ba'a karaba ba ba daya bane da an sace''.

Tuni dai kungiyoyin da ke yaki da cin hanci da rashawa wadanda suka kasance yan gaba-dai gaba-dai wajen matsin lamba a bincika lamarin suka ce da sake, kamar yadda Malam Sani Aliyu na kungiyar fafutukar yaki da cin hanci da arshawa da tabbatar da dimukurdiyya ya bayyana.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Pinado Abdu Waba