Ceto wadanda ke cikin mawuyacin hali
A shekarar da ta gabata an ceto bakin haure da dama daga halaka a kokarinsu na shiga nahiyar Turai ta tekun Bahar Rum. Jirage ruwa na hukumomi da na masu yin sana'ar su ne ke shigewa gaba wajen yin wannan aikin ceton.
Gab da kaiwa tudun mun tsira
Wannan jirgin ruwan na dab da kai 'yan cirani tudun mun tsira, wannan shi ne daidai abinda 'yan ciranin ke fassarawa da "Jaguar" a cikin teku. Irin wadannan jiragen ruwan da ba na hukuma ba kan kai kaya na tonon mai ne a teku.
Masu aikin cetoi da ke zaman kan su
Ana kara samun bukata ta ceton 'yan cirani da jiragen ruwa da ke sintiri irin na Amirka mai suna "Jaguar". To sai dai a nan Turai akwai karancin irin wadannan jirage musamman ma ga shirin na "Triton" da ke nema da ceton bakin haure a kan tekun Bahar Rum, sai dai aikin wannan shiri ba ya gota kilmoita 56 daga gabar ruwan Italiya.
Rashin samun kariya a Teku
Daga watan Disamba da ya gabata zuwa yanzu an ceci 'yan cirani 1,500 daga jirginsu da ke kokarin nutsewa sau biyu kuma wani kamfanin Jamus da ke samar da abin tonon mai na cikin ruwa mai suna Christopher Opielok ne ya yi hakan, sai dai sauarn jiragen ruwa neman ceto ba su samu yin hakan ba.
Bada tallafin da ba zai je ko ina ba
Jirgin da ke jigilar kaya na aikin tonon mai daga kasar Malta zuwa Libya yanzu haka kan yi tanadin kayan abinci da barguna da magunguna da nufin bada shi tallafi ga 'yan cirani.
Rashin tabbacin rayuwa bayan ceto
Duk da cewar jirgin ruwa kamar "Jaguar" na kasar Amirka kan ceci 'yan cirani daga halaka a teku, hakan ba ya na nufin sun tsira ba ne domin tsananin sanyi kan hallaka wasunsu 'yan mituna da cetonsu kamar yadda Opielek ya nunar. Galibi bayan ceto a kan kidaya wadanda ke da sauran shan ruwa nan gaba.
Tallafa wa jiragen da ke daf da kifewa
Matuka jiragen ruwa musamman wadanda ba na gwamnati ba kan taimaka wa jiragen 'yan cirani da ke cikin yanayi na bukata ko kuma suka kama hanyar kifewa. Hakan kan wakana ne a hanyoyin da ake bi don kai kayayyaki gabar ruwan Libya.
Daukar tsawon lokaci kafin aikin ceto
Kamar yadda ake gani a wannan hoton, 'yan cirani na yin iyo don kaiwa gabar kogi sakamakon kifewar jirginsu. Jirgin nan na "Jaguar" kan taimaka wajen ceto mutane kana ya sanar da masu sintiri na gabar ruwan Italiya. Mafi akasari a kan dau tsawon sa'o'i 24 kafin jami'an na Italiya su kai ga yin aikin ceto.