Shugaban Chadi na yakar Boko Haram
April 6, 2020A wani taron maneman labarai da ya yi, Shugaba Idriss Deby Itno na Chadi ya ce ya kawo karshen 'yan ta'adda a kasarsa, inda ya ce a yanzu babu ko guda kuma shi kadai ya yi wannan yakin ba tare da kasashe mokwaftansa ba, inda ya ce: "Babu Boko Haram ko guda yanzu a kasar Chadi, mun kwace dukkanin yankunanmu. Sai dai tun da muka fara wanan yunkurin, kasar Chadi ita kadai ta yi wanan yakin."
Yabon gwani ya zama dole
Hassane Bello, daya daga cikin 'yan kungiyar farar hula na yankin Diffa ya bayyanawa DW cewa sun yaba da wannan yunkuri, koda yake ya ce ba su ji dadin rashin saka hannun kasashe makwabtan Chadin ba. Mazauna Diffan dai sun san za a yi hakan, ganin yadda aka yi wa kasar Chadi barna. A hannu guda kuma gwamnatin Jamhuriyar Nijar ita ma ta shirya da nufin kakkabe sauran tsirarun mayakan Boko Haram din da suka shiga kasar da kuma kare dukanin iyakokinta.