Chaina: Amirka da Koriya ta Arewa ku taka wa juna birki
August 15, 2017Talla
Mista Yi ya fadi hakan ne a yayin zantawarsa da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov ta wayar tarho a wannan Talata, a lokacin da suke nazari kan takaddamar da ke a tsakanin kasashen Amirka da Koriya ta Arewa kan batun gwajin makami mai linzami. Wannan na zuwa ne bayan da kasar Chaina ta sha alwashin daukar mataki idan har Amirka ta kaddamar da matakan da za su kawo illa ga harkokin kasuwancin kasashen biyu.
Kasar ta Amirka dai ta soma wani bincike da ya shafi kasar ta Chaina kan batun mallakar kirkire-kirkire, inda Amirkan za ta duba batun ko siyasar kasuwanci ta kasar ta Chaina na kawo wata illa ga kamfanonin kasar ta Amirka musamman ma a fannin ilimin kirkire-kirkire, inda ake sa ran Amirkar za ta kakaba wa Chaina wasu takunkumai.