1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 100 da kafa jam'iyyar CCP a Chaina

Binta Aliyu Zurmi MAB
July 1, 2021

An gudanar da bikin cika shekaru 100 da kafa jam'iyyar kwaminisanci a kasar Chaina a dandalin Tiananmen da ke Beijing fadar gwamnatin kasar bisa jagorancin shugaban kasa Xi Jinping .

https://p.dw.com/p/3vqi8
China I Amsprache Präsident  Xi Jinping
Hoto: Ng Han Guan/AP/picture alliance

A wannan rana ta Alhamis ce jam'iyyar Kwaminisanci mai mulki a kasar Chaina ta cika shekaru dari da kafuwa. A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a gagarumin taron da ya gudana a dandalin Tiananmen da ke Beijing fadar gwamnatin kasar, shugaban kasa Xi Jinping ya jinjina wa 'yan kasar bisa ci gaba da turje wa duk wata barazana daga kasashen ketare.

Shugaban ya jaddada wa mahalarta taron sama da mutum dubu 70 cewar lokacin yi wa chaina barazana da kuma raina mata wayo ya wuce har abada, kuma duk wanda ya yi kokarin yin wani abu da ba su aminta da shi ba za su saka kafar wando daya da shi.

A shekarar 1921 Mao Zedong tsohon shugaban kasar ya kafa jam'iyyar wacce shugaban kasar Chaina na yanzu ya ce ta fidda miliyoyin al'ummar kasar daga talauci, yanzu haka dai Xi Jinping ya kasance shugaba mai cikakken iko, kamar yadda aka gada daga karantarwar Mao Zedong.