Dan rajin kare hakkin bil'adam zai fuskanci dauri
July 29, 2019Talla
Huang mai shekaru Hamsin na zaman kaso a gidan yarin kasar tun shekara ta 2016 bayan sanya masa takunkumin siyasa har na tsawon shekaru hudu, almarin da Majalisar Dinkin Duniya da wasu kungiyoyin hakkin 'dan Adam da kuma mahaifiyarsa suka bayyana rashin jin dadinsu a kai.
Kafin tsare shi 'dan gwagwarmaryar ya yi fice a fagen nemarwa wadanda aka raba da muhallansu hakkinsu, ciki har da mutanen da girgizar kasa ta shafi muhallansu a Kudu masi Yammacin yankin Sichuan tun shekarar ta 2008 .