1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China na tallafawa Gini wajen yakar Ebola

August 17, 2014

Likitocin kasar China sun isa Gini domin tallafawa jami'an kiwon lafiyar kasar wajen yaki da cutar nan ta Ebola da ta yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama a kasar.

https://p.dw.com/p/1Cw1T
Ebola
Hoto: Reuters

Likitocin guda uku wadanda kwararru ne a fannin kula da lafiyar al'umma za su maye gurbin wasu takwarorinsu ne da suka shafe tsawon lokaci suna gudanar da aiki a wannan kasa.

Wata majiya ta ma'aikatar lafiyar kasar ta Gini dai ta ce likitocin na China za su yi aiki kafada da kafada ne da likitocin Gini inda za su agaza musu musamman da dabaru na dakatar da bazuwar cutar kazalika za su yi wa kananan jami'an kiwon lafiyar kasar horo na kare kai daga kamuwa da cutar yayin jinyar masu dauke da ita.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu