1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren Saudiya a Yemen na kara ta'azzara

Lateefa Mustapha Ja'afarApril 13, 2015

Kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar al'ummar kasar Yemen su kara shiga halin tasku wanda ya hadar da karancin abinci.

https://p.dw.com/p/1F7Gi
Hoto: DW/Saeed Alsoofi

Wannan gargadi dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da hare-haren jiragen saman yaki da kasar Saudiya ke ci gaba da jagorantar kaiwa a kan 'yan tawayen Huthi da suka kawace iko da babban birnin kasar Sana'a. Kasar ta Saudiya dai na zargin Iran da taimakawa 'yan tawayen na Huthi da ke zaman Musulmi mabiya Shi'a, inda ta nemi agaji daga kawayenta na yankin gabas ta tsakiya wajen farwa 'yan tawayen. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ma dai ya yi makamancin wannan gargadin inda ya ce karuwa rikicin na kara jefa a'lummar kasar cikin garari tare kuma da lalata kayayyakin more rayuwa. A hannu guda kuma a yau ne aka rantsar da Khaled Bahah a matsayin sabon mataimakin shugaban kasar ta Yemen a ofishin jakadancin kasar da ke birnin Riyadh na Saudiya. An dai rantsar da Bahah a gaban Shugaba Abedrabbo Mansour Hadi na Yemen din da a yanzu haka ke yin gudun hijira a Saudiyan.