Ci gaban diflomasiyya ga 'yan adawar Siriya
March 26, 2013A karon farko, wakilan 'yan adawar Siriya sun hau bisa kujerar wakilcin kasar a lokacin taron kungiyar kasashen Larabawar daya fara gudana - wannan Talatar a daular Qatar, lamarin da ke zama ci gaba ne ta fannin diflomasiyya ga fafutukar da 'yan adawar ke yi na kawar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad. Tawagar 'yan adawar a karkashin jagoracin Mouaz al-Khatib, tsohon shugabanta ta shiga zauren taron ne yayin da ake mata tafi, kana ya zauna a kujerar da kungiyar ta warewa Siriya ne a bisa gayyatar sarkin daular Qatar Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani.
Dama tun a makon jiya ne taron ministocin kula da harkokin wajen kasashen Larabawa ya bayar da shawarar mikawa 'yan adawar gurbin kasar ta Siriya a cikin taron. A jawabin daya yi, sarkin na Qatar, mai masaukin baki, ya ce 'yan adawar sun cancanci sabon matsayin bisa karbuwar da suke ci gaba da samu a ciki da wajen kasar ta Siriya.
Idan za'a iya tunawa dai tun a shekara ta 2011 ne kungiyar kasashen Larabawar ta dakatar da wakilcin gwamnatin Siriya a cikin ta bisa abinda ta ce gallazawar da take yiwa masu boren nuna adawa da ita.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou