1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci-gaban sauraron shari'ar Breivik

April 18, 2012

Anders Behring Breivik ya amsa laifin kashe mutane 77 a kasar Norway a watan Yulin shekarar 2011

https://p.dw.com/p/14fwB
Defendant Anders Behring Breivik answers questions made by the public prosecutor Bejer Engh (not pictured) at the start of the third day of proceedings in the courthouse in Oslo April 18, 2012. Breivik, who killed 77 people, said at his trial on Tuesday his shooting spree and bomb attack were "sophisticated and spectacular" and that he would do the same thing again. REUTERS/Fabrizio Bensch (NORWAY - Tags: CRIME LAW SOCIETY POLITICS)
Hoto: Reuters

A yau, 18.04.2012 ne a birnin Oslo na kasar Norway aka ci gaba da sauraron shari'ar da ake wa Anders Behring Breivik da ya aikata kashe kashen ba gaira ba dalili a wancan shekara tare da neman sanin ko shin da wata hulda da ke akwai tsakaninsa da kungiyoyin masu raya manufofin NAZI. Su dai lauyoyin kasar a yanzu suna mai da hankali ne akan lokacin da ya shude tsakanin 2001 zuwa 2006 wanda lokaci kenan da Breivik ya fara nuna kyama ga manufar cudanya tsakanin al'umomi masu aladu dabam-dabam musamman ga Musulmi.

Breivik ya ce ya yi amfani da hanyar Internet wajen samun abokan hulda da ke da ra'ayi irin nasa. Shi dai Breivik ya ki ya amsa wasu tambayoyi da aka yi masa yayin zaman kotun na yau. To amma ya yi ikirarin kai harin da ya halaka mutane 77 a watan Yulin shekarar 2011 yana mai cewa yin hakan wani matakin tsaro ne na gaggawa da ya dauka bisa tsoron da yake yi cewa al'umar Norway za ta rungumi Musulunci.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu