Kyamar tubabbun 'yan Boko Haram
July 9, 2019Hukumomi sun fuskanci kalubalen saboda zaman doya da manja da ake samu wanda ta kai ga ana farautar wadan bayin Allah da su ka tuba daga ta'asar da su ka yi su ka kuma rungumi zaman lafiya.
Wadansu da dama kuma da rikicin Boko Haram ya rabasu da matsugununsu na kallon tsoffin dakarun na Boko Haram a matsayin wadanda ka jefa su a cikin bala'in da suka samu kansu ciki na bakar wahala da suke sha a halin yanzu.
Muhammad Bello wanda aka fi sani da Gabage wani tsohon jojan Boko Haram ne da ya tuba aka ba shi horo kuma ya koma cikin mutanen garinsu ya bayyana irin kyama da barazana da ya ke fuskanta shida sauran ‘yan uwan sa.
Bisa wannan ne ya sa aka shirya bude wata cibiya a Maiduguri domin sake koyar da irin wadannan tubabbun Boko Haram kan yadda za su zauna cikin al'umma.
Sai dai masana da masharhanta na bayyana irin kalubalen da wannan cibiya ke fuskanta wanda yawanci ke ganin ba bude cibiyar ake bukata domin mayar da wadan nan bayin Allah zuwa garuruwansu ba.
Su ma mutanen gari sun nuna damuwa tare da neman hukumomi su sake fasali na wannan shiri tare da ilmantar da al'umma kan yadda za su karbi irin wadan mutane.
Masharhanta dai na fatar samun tsari da zai inganta wanda ake da shi domin bada kofa ga ‘yan bindigar da ke son ajiye makamai su samu kwarin gwiwar komawa garuruwansu ba tare da tsangwama ko fuskantar wata barazana ba.