Cigaba da neman goyon bayan na yakar Siriya
September 11, 2013Obama ya ambata hakan ne a wani jawabi da ya yi ga al'ummar kasar jiya ta gidan talabijin, inda ya ce shaidun da suka samu sun nuna cewar an yi amfani da makamai masu guba a kasar musaman ma dai wanda ke dauke da sinadarin na Sarin da ke kashe laka, a saboda haka ya ce bai kamata duniya ta zuba ido tana kallo wannan karen tsaye ga al'ummar kasar ba.
Shugaba Obama ''idan masu mulkin kama karya suka aikata ta'asa irin wannan, suna son kasashen duniya su kau da idanunsu. Tambaya a nan ita ce shin me Amirka da sauran kasashen duniya suka shirya yi dangane da wannan batu. Idan muka ki daukar mataki, gwamnati Assad za ta yi amfani da wannan dama wajen cigaba da amfani da makamai masu guba''.
To sai dai a daura da wannan, Obama ya yi maraba da shirin kasar Rasha na kira ga gwamnatin Assad da ta mika makamanta masu guba.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu