Najeriya: Badakalar cin hanci a fannin tsaro
May 28, 2018Kungiyar ta Transparency International da ta kaddamar da rahoto kan wani bincike da ta gudanar mai zurfi ta ce ta bankado zargin tafka cin hanci da rashawa a makudan kudin da ake ware wa fannin tsaro a Najeriyar da yawansu ya kai sama da Naira bilyan 241 a kowace shekara, kuma abin karuwa yake. Kungiyar ta ce almundahanar ana yin ta ne kama daga matakin gwamnatin tarayya zuwa jihohi, domin kuwa a cewarta rahoton ya gano cewa jihohi 29 na Najeriya sun gaza bayanin yadda suka kashe dalar Amirka miliyan 580 da suka karba da sunan harkokin tsaro a shekara guda. Rahoton ya kuma gano yadda ake karkatar da wadannan kudade ta hanyar yakin neman zabe, sannan ana zargin jami'an gwamnati na zuba sauran a aljihunsu.
Karkatar da kudin zuwa ma'aikatun da ba su da alaka da tsaro
Abin da ya fi daga hankali a rahoton shi ne yadda wasu hukumomin da basu da alaka da tsaro a Najeriyar ke karbara wadannan kudade a yanayi na a bi yarima a sha kida, biyu daga ciki da aka, ambato su ne hukumar kula da harkokin yawan bude idanu da makarantar koyon aikin hakora. A binciken nasu sun gano cewa an samu karuwar wadannan kudade da akan kebe a shekarar 2017 da ta gabata da ma kasafin kudin wannan shekara, bayan kuwa an samu raguwar su a farkon shekara ta 2016 a karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. A ta bakin Katherine Aitken mai ba da shawara a fannin tsaro ga kasashen Afrika da ke ofishin jakadancin Birtaniya wannan rahoto muhimmin ci gaba ne na binciken da aka yi a kan yadda ake tafiyar da kudaden sashin tsaro a Najeriya da suka zama wata kafa ta tafka cin hanci da rashawa a dai-dai lokacin da Najeriyar ke fuskantar kalubale a sashin tsaron, ta kuma yi fatan cewa binciken zai samar da wata kafa ta gudanar da sauye-sauye da zai samar da kyakkyawar makoma. Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki ta bakin wakilinsa ya ce za su yi nazari a kan wannan rahoto domin majalisar ta dauki matakin da ya dace.