Cin hanci da karbar rashawa a kasar Kenya
January 31, 2006Bankin Dunia ta yanke shawara kin zuba wasu kuddaden bashi, da su ka kai kimanin dalla million 260 ga kasar Kenya.
Bankin ta dau wannan mataki bayan ta samu rahotani cikkaku masu nuna cin hanci da rashawa a kasar, sun kai matsayin lahaula.
Banki Dunia ta amince bada wannan kudaden bashi ga Kenya tun shekara ta 2004.
Za ayi anfani da su ta hanyar yaki da cutar Sida, kyauttata harakokin illimi da kuma inganta tafiyar da ayyukan bankunan kasar.
Hukumomin Bankin Dunia sun bayyana cewa ba za su bada wanan kudade ba sai in gwamnatin shugaban Maw Kibaki ta nuna cikkakun alamomi na yaki da cin hanci da rashawa da ke matsayin annoba a wannan kasa.
A yanzu haka,akwai wata tawaga da Bankin ta tura a kasar Kenya, domin gani da ido, yadda a ke ciki, a game da yaki da ci hanci da karbar rashawa.
Matakin na Bankin Dunia, ya zo kwana daya rak, bayan da wani bincike ya gano cewar, gwamnatin Kenya ta kashe magudan kudade da yawan su, ya kai dalla kussan million 13, wajen sayen motoci na kawa, a yayin da al` ummar kasa ke fama da bala´in talauci da na yinwa.