1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin hanci yayi katutu a tsakanin jami´an gwamnatin Kenya

February 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bv8R

´Yan majalisar dokokin Kenya wadanda suka yiwa tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na kasar tambayoyi sun ce sun kadu da shaidar da ta yi zargin cin hanci da rashawa a cikin gwamnati. ´Yan majalisar dokokin dai sun yi wa John Githongo tambayoyin ne a birnin London a dangane da zargin yin almundahana tsakanin manyan jami´an gwamnatin Kenya. Mista Githongo ya zargi ministocin gwamnati da yin sace miliyoyin daloli. Githongo ya ce ba zai iya ba da wannan shaida a cikin Kenya ba saboda barazanar da ake yiwa rayuwarsa. A halin da ake ciki shugaban Kenya Mwai Kibaki ya ba da umarnin gudanar da bincike akan mutane 14 da aka zarga da hannu dumu dumu a wannan abin kunya.