Amirka ta tsawaita dokar nesa-nesa da juna
March 30, 2020Da farko dai shugaban ya so ya sassauta dokar a tsakiyar watan Afrilu don 'yan kasar su sami damar gudanar da ayyukansu kamar yadda aka saba. Sai dai kuma bunkasa da cutar Corona ta yi a kasar a baya-bayan nan ya girgiza kasar.
Gwamnatin Amirka ta ce tsawaita dokar kulle din ya zama wajibi domin masana sun yi hasashen Corona na da karfin da za ta iya kashe mutane 200,000 kuma miliyoyin jama'a ka iya kamuwa daga wannan annoba a Amirka.
Kawo safiyar Litinin din nan Amirka na da sama da mutum 140,000 da suka kamu da Coronavirus, adadin da ya zarta na kowace kasa a duniya. Hakan na nufin Amirka ita ce ta farko a jerin kasashe 199 da ke dauke da cutar ta Corona. Cutar ta kuma kashe akalla mutane 2,488 a kasar kawo yanzu.
Coronavirus dai ta fara bulla a Amirka a ranar 20 ga watan Janeru na shekarar 2020 kuma tun daga lokacin cutar ke ta bazuwa musamman a birnin New York inda ta kashe sama da mutum 1,000 a cikin kwanaki tara.