1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona: Amirka ta yi gargadi kan shiga Jamus

November 23, 2021

Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta gargadi Amirikawa kan su dakata da shiga Jamus saboda kamarin da annobar corona ta yi a kasar.

https://p.dw.com/p/43MC7
SRAS-CoV-2 l Covid-19, Mikroskopische Aufnahme
Hoto: IMAGE POINT FR - LPN /BSIP/picture alliance

Wannan gargadin na zuwa ne bayan da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Amirka ta fitar da sanarwar tabbatar da yin cikakken rigakafin annobar corona idan ya wajabta ga mutum ya shiga Jamus din. 

A farkon wannan watan ne dai kasar ta Amirka ta bude iyakokinta, bayan sanya dokar hana tafiye-tafiye zuwa kasashen waje na tsawon shekara daya da rabi.

Jamus da ke zama kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Turai na fuskantar barazanar cutar a karo na hudu, inda asibitocin kasar ke cika da masu dauke da cutar fiye da yadda aka gani a bara, lamarin da aka danganta shi da jan kafa wurin yiwa al'umma rigakafin annobar.

Tuni dai aka sanya kasashen Denmark da Beljiyam da Hungari da Austiriya da Netherlands cikin jerin kasashen da cutar ta kamarin gaske.