Covid-19: Nijar ta dau sabbin matakai
March 28, 2020Daga cikin manyan matakan da hukumomin Jamhuriyar nijar suka dauka har da na takaita zira-zirgar jama’a daga karfe bakwai na yamma zuwa shida na safe, tare da killace Yamai babban birnin kasar ba fita ba shiga.
A jawabin da ya yi wa 'yan kasar shugaba Mahamadou Issoufou ya bayyanan cewa "a kara addu’o’i a duk fadin kasar, da ayyana dokar ta baci ta kiwon lafiya a fadin kasar ta Nijar tun daga jiya Juma’a, da dokar takaita zirga-zirga a birnin Yamai ta tsawon makonni biyu, dokar da ake iya sabuntawa, ganin cewa har yanzu a Yamai ne wannan cuta ta ke. Sannan da killace birnin Yamai ba shiga ba fita daga wannan Lahadi 29 ga wannan wata na Maris, daga misalin 12 na dare"
Shugaban na Nijar ya kuma sanar da yafe kudaden biyan wuta da ruwa na watanni biyu ga masu karamin karfi da kuma yin afuwa ga ‘yan kaso da yawansu ya kai mutun 1,547 a wani mataki na rage cinkoso a gidajen kason kasar ta Nijar sakamakon cutar ta Coronavirus.