Majami'u na koka wa da Corona
September 5, 2020Matakan da ke da nasaba da annobar corona da duniya ke ciki, sun janyo rashin kudade ga wasu majami'u musamman a kasashe irin su Yuganda da Zimbabuwe da kuma Najeriya.
Tuni ma wasu jagororin addinin Kirista a Yuganda, suka kaddamar da wani kamfe da ke nuna cewa an tauye musu damar numfashi, suna masu cewa matakai ne da za su taba karfin imanin mabiyansu.
Wani fitaccen limamin Kirista a Najeriya, Fasto Chris Oyakhilome, ya kalubalanci shugabannin gwamnati kan debar musu sa'o'i da ake yi domin gudanar da ibada.
Wasu rahotannin daga Najeriya sun ce ta kai wasu majami'u sun umurtar mabiyya da su rika zuba kudaden zakka ta hanyar asusun bankuna.
A watan jiya ne aka koma zuwa majami'u a Najeriyar, inda aka ba da sa'a guda kacal.
A Tanzaniya kuwa Shugaba John Magufuli ne ya bayar da shawarar amfani da addu'o'i ga jami'an lafiya don kawo karshen annobar.
Addini dai na da matukar karfi da tasiri a rayuwar al'umar nahiyar Afirka.