1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adadin wadanda Corona ta yi sanadiyyar ajalisun sun karu

Abdoulaye Mamane Amadou
April 27, 2020

Adadin wadanda annobar Corona ta yi sanadiyyar ajalisun sun kai dubu 206 da 567 a duniya kamar yadda wasu alkaluman bincike da kamfanin AFP ke tattarawa ya nuna.

https://p.dw.com/p/3bTwl
Coronavirus Brasilien Porto Alegre Intensivstation für Covid-19 Patienten
Hoto: AFP/S. Avila

Kididdigar ta nuna cewa baya ga wadanda suka mutu, wasu fiye da mutun miliyan 2. 96. 540 sun kamu da cutar a kasashe 193 tun bayan bayyana bulluwarta a duniya.

Amerika ita ce ke kan gaba ya zuwa yanzu da wadanda cutar ta fi yiwa kisan mumuke, inda ta ke da mamata fiye da dubu 54 da 800. Italiya na da mamata akalla dubu 26 da 644. Spain dubu 23 da 521 a yayin da Faransa ke da mamata fiye da dubu 22 da 800 sai Birtaniya mai mata dubu 20 da 732.

Alkaluman kamfanin sun kuma ce nahiyar Afirka a yanzu ita kadai ce cutar take da dan sauki-sauki inda aya zuwa yanzu akalla mutum dubu 1.425 suka hallaka daga cikin mutun fiye da dubu 32 da suka kamu da Corona.