Corona ta shiga Majalisar Dokokin Botswana
April 9, 2020Talla
Wannan ya biyo bayan mu'amulla da suka yi da wata jami'ar kiwon lafiya wace a wannan Alhamis aka gano cewa tana dauke da Coronavirus.
A yayin da yake jawabi a gaban majalisar dokokin kasar, ministan lafiyar kasar, ya ce yana sanar da duk dan majalisar da ke wurin cewa wajibi ne daga wurin su kama hanya zuwa wurin kebe kansu. A ranar Laraba ce dai 'yan majalisar da shugaban kasar ta Botswana suka hadu a zauren majalisar kuma suka yi mu'amulla da ita wannan mai Coronavirus.
Wannan shi ne karo na biyu da Shugaban Kasar Mokgweetsi Masisi ta Botswana zai kebe kansa. A watan da ya gabata ya yi makonni biyu a kebe bayan da aka yi zullumin ya yi mu'amulla da mai Coronavirus.