1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Daukar matakai kan Coronavirus

Gazali Abdou Tasawa
January 27, 2020

Firaministan Chaina Li Keqiang ya kai ziyara a birnin Huwan inda aka fara samun yaduwar cutar Coronavirus da kawo yanzu ta kashe mutane 80, yayin da wasu kusan 1,800 suka kamu da kwayoyin cutar a kasar.

https://p.dw.com/p/3Wr1e
China Coronavirus l Anreise eines medizinischen Teams in Zhengzhou, Provinz Henan
Hoto: Imago images/Xinhua/L. Jianan

Gwamnatin kasar dai ta ce Firaminista Li ya kai ziyarar ne a babban birnin jihar Hubei ta tsakiyar kasar, domin ganewa idanunsa irin matakan da hukumomin yankin suka dauka domin tunkarar annobar da ba su shawarwari, ya kuma gana da marasa lafiya da likitoci a sansanononin da aka kebe domin kula da mutanen da suka kamu da kwayar cutar ta Coronavirus.

 Wannan dai shi ne karo na farko da wani daga cikin kusoshin gwamnatin kasar ta Chaina ya ziyarci birnin na Huwan tun bayan bullar annobar kwayar cutar ta Coronavirus.