Coronavirus da canjin yanayi : Canje-canje guda bakwai ake sa ran samu
Daga kara gurbacewar iskan da ake shaka, zuwa bazuwar halitun da ke rayuwa a gewayen birane, matsalar Coronavirus za ta bar tabo a kan sha'anin kare muhali.
Iskan da ake sha'a mafi kyau
Yayin da duniya ta tsaya, kwatsam dakatar da ayyukan masana'antu ya rage gurbataccen iska. Hotunan tauraron dan Adam sun nuna yadda aka rage samun dioxid(NO2) iskan gas mai guba, wanda injuna motoci da na kamfanoni ke saki a cikin birane abin da ke janyo gurbacewar iskan da ke cikin sararri.
Iska mai guba na CO2 ya ragu
Iska mai guba kamar na NO2 da carbon dioxide da CO2 duk sun ragu saboda annobar Coronavirus. Da zaran al'amuran tattalin arziki sun tsaya, iska mai guba na C02 na raguwa. Lamari na baya-baya da ya faru shi ne na matsalar tattalin arziki da aka yi faman yi tsakanin shekara ta 2008 zuwa 2009. A China kawai an samu raguwar iska mai guba da kishi 25 cikin dari. Sai dai na wani dan lokaci ne.
Wata sabuwar duniya ta halitun da ke rayuwa a gewayen birane
Yayin da jama'a suka kasance a gida wasu halitun da ke rayuwa a gewaye da birane na more wa wannan dama. Misali dakatar da yawan zirga-zirgar motoci yakan sa kananan halitu kamar su bishiya su tsallaka titi babu fargaban motocin za su take su. Yayin da wasu kamar su agwagwa za su rika azawa kansu ayar tambaya ina jama'a ta shiga, don haka dole su nemi wasu hanyoyi na samun abinci.
Jan hankali a kan cinikin dabobbi daji a duniya
Masu fafutukar kare muhali na ganin annobar Coronavirus za ta taimaka a daina kasuwancin dabobbin dajin, abin da ke zaman dalili na kai ga bacewar wasu halitun a doron duniya. COVID 19 kamar yadda ake hasashe ta samo asili ne daga wata kasuwa a Wuham inda ake yin cinikin dabobbin daji da ransu. Haramta yin kasuwancin dabobbin dajin da ransu zai iya zama wata hanya ta magance matsalar.
Hanyoyin zirga-irga na ruwa sun kasance da kyau.
Lokaci kadan bayan Italiya ta ba da sanarwa kaddamar da dokar hana zirga-zirga, an yi ta nuna hotuna a duniya yadda ruwan teku Italiya suka yi haske. Saboda babu jiragen ruwa da ke kai da kawo yadda suka saba. Ruwayen tekun sun samu raguwar gurbata, haka ma halitun da ke cikin ruwan.
Sharar ledoji ta karu
Ba dukka labarin ne ke da dadin ji ba. Abu mafi muni ga sha'anin kare muhali da Coronavirus ta janyo shi ne karuwar ledojin da ake yin amfani da su sau daya. Kayan likita kamar su safar hanu ta roba da sauran kayayakin, da kuma yadda yanzu da sannu a hankali mutane ko abinci suka saya sun gwamace a nade musu shi cikin ledojin roba, domin dakile yaduwar annobar Coronavirus.
A yanzu ana yin fatali da irin matsalar da canjin yanayi ka iya haifarwa
Sakamakon kamari da COVID 19 ta yi, an dage taron tattaunawa kan canjin yanayi. Kwararru sun yi kashedin cewar ka da a yi jinkiri wajen daukar muhimman shawarwari a kan canjin, duk da cewar an dage taron Majalisar Dinkin Duniyar kan sauyin yanayin har sai shekara ta 2021. Ko da shi ke ma an samu raguwar iska mai guba saboda annobar ta Coronavirus. Za a iya samu canji yanayi na gaba daya a gaba.