Coronavirus: Karuwar sabbin kamu a Jamus
April 28, 2020Shugaban cibiyar yaki da cutattuka masu yaduwa ta Jamus ya bukaci al'umma su ci gaba da bin dokokin da aka tsara don sassaunta yaduwar cutar coronavirus bayan da wasu alkaluma suka nuna har yanzu ana samun wadanda ke kamuwa da cutar a cikin kasar.
Lothar Wieler shugaban cibiyar yaki da cutattuka masu yawa ta Robert Koch, yayin wani jawabi da ya yi a Berlin ya jaddada muhimmancin bin dokokin bada taraza da kuma amfani da kyalen rufe baki da hanci.
"Yace kawo yanzu mun yi kokarin dakile annobar baki dayan mu, kuma wannan hadin kai ya na da muhimmanci a gare ni. To amma kwayar cutar za ta cigaba da kasancewa tare da mu tsawon watanni, amma dai muna iya cewa mun yi nasara."
Dukkanin jihohi 16 na tarayyar Jamus sun sanya dokar tilasta amfani da kyalen rufe baki da hanci yayin dukkan wata mu'amala a bainar jama'a kamar zuwa kantuna da shiga motar haya.