Tsauraran matakai ga masu cutar Corona a Italiya
March 10, 2020Gwamantin kasar Italiya ta dauki matakin killace 'yan kasar har zuwa ranar uku ga watan Afrilu a wani mataki na dakile yaduwar cutar Covid19 da ke ci gaba da kamari.
Shugaban gwamnatin kasar Giuseppe Conte, ya tabbatar da dokar tabacin wacce ake sa ran za ta takaita shige da ficen 'yan kasar kimanin miliyan 60 a wani yunkuri na kawar da cutar daga kasar wacce ta ke ta farko a nahiyar Turai mafi kamuwa da Corona Virus.
Dokar ta kuma bayyana matakin soke duk wasu tarukan jama'a, da dukkan wasannin motsa jiki, tare da mayar da wuraren wasannin a matsayin asibitocin wucin gadi ga masu wasannin motsa jikin da aka samu sun kamuwa da cutar.
A gefe daya kuwa shugaban kasar China Xi Jinping ya kai wata ziyarar ba zata a yankin Wuhan da ke zama yankin da cutar ta Covid19 ta samo asali a wani mataki na gane wa idonsa halin da yankin ya ke ciki, inda daukacin yankin ke killace tun a karshen watan Janairun wannan shekarar ta 2020.
Rahotanni sun ce wannan ziyarar ita ce irinta ta farko tun bayan kwararan matakan da kasar ta dauka na dakile cutar wanda ake cewa ya na yin tasiri.