1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina: Raguwa da karuwar Coronavirus

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 17, 2020

Hukumar kula da lafiya ta kasar Chaina ta bayyana cewa kawo yanzu adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da kwayar cutar Coronavirus ya kai 105, yayin da sama da mutane dubu 70 suka kamu da cutar.

https://p.dw.com/p/3Xu9e
China | Coronavirus
Hoto: picture-alliance/dpa/XinHua/Z. Yuwei

Baki daya dai mutane 1,800 ne suka rasa rayukanasu sakamakon wannan cuta da ke saurin yaduwa a Chainan, yayin da adadin mutanen da suka kamu da ita ya karu da sama da 2000, inda yawan masu dauke da cutar a yanzu haka ya kai dubu 70 da 500. Koda yake za a iya cewa a kwanakin baya-bayan nan adadin yaduwar cutar ya ragu, in banda a Lardin Hubei da ke zaman tushen Coronavirus din. Sai dai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta yi gargadin cewa ba girin-girin ba dai ta yi mai.