Amirka ce kan gaba a yawan masu corona
March 31, 2020Talla
Yawan mutanen da suka rasu sakamakon annobar cutar coronavirus a Amirka ya haura yawan wadanda suka rasu a Chaina inda adadin ya kai mutum 3,300 kamar yadda alkaluma da jami'ar Johns Hopkins ta fitar ya nuna.
Gwamnan Jihar New York Andrew Cuomo ya ce ana bukatar ma'aikatan lafiya kimanin miliyan dayadomin taimkawa wajen yaki da cutar.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ja hankali da cewa yayin da hankula suka karkata ga yammacin Turai da kuma Arewacin Amirka inda cutar ta fi tsanani, har yanzu lamarin bai kare ba a nahiyar Asia
Dr Takreshi Kasai daraktan shiyya na hukumar lafiya ta duniya WHO ya ce za a dauki lokaci mai tsawo ana fama da cutar.