1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutum guda ya mutu a kasar Philippines

Zulaiha Abubakar MNA
February 2, 2020

Hukumar lafiya ta kasar Philippines ta sanar da mutuwar wani mutum mai shekaru 44, dan asalin garin Wuhan da ke kasar Chaina bayan ya sha fama da takaitacciyar jinya.

https://p.dw.com/p/3X9V6
Philippinen Coronavirus Schutzmaskenverkauf
Hoto: Getty Images/AFP/T. Aljibe

Wannan al'amari ya sanya jami'an kiwon lafiya a kasar ta Philippines gudanar da gwajin gaggawa a kan wata mace mai shekaru 38, wacce suka shigo kasar tare da mamacin daga Chaina, kuma tuni sakamakon gwajin ya tabbatar da tana dauke da kwayar cutar Coronavirus. Yanzu haka dai hukumar lafiyar kasar ta killace ta a babban asibitin birnin Manilla.

Wannan shi ne karo na farko da wani ya mutu a wajen kasar Chaina tun bayan billar cutar. Yanzu haka shi ma Shugaba Rodrigo Duterte na kasar ta Philippines ya bi sahun takwarorinsa na kasashen ketare wajen dakatar da tafiye-tafiye tsakanin al'umma da nufin hana cutar ta Coronavirus yaduwa.