'Yan majalisar wakilan Najeriya sun janye aniyarsu ta dage zamansu tare da dakatar da ayyukansu har sai nan da makonni biyu, biyo bayan matsin lamba daga al'ummar kasar. Majalisar dai ta ce za ta dage zamanta saboda samun mutum guda da ke dauke da cutar Coronavirus.