1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Coronavirus: Ana ci gaba da binciken gano magani

Ramatu Garba Baba
March 31, 2020

Annobar Coronavirus na ci gaba da lakume rayuka a yayin da masana kimiya ke fadi tashin gano riga-kafi ko maganin cutar da ke kokarin durkusar da tattalin arzikin duniya da jefa jama'a cikin kuncin rayuwa.

https://p.dw.com/p/3aH1Q
Spanien Badalona | Coronavirus | Intensivstation Krankenhaus
Hoto: picture-alliance/AP Photos/A. Surinyach

Ma'aikatar lafiya a kasar Burundi ta ce an gano wasu mutum biyu da suka kamu da cutar, daya ya shigo kasar daga kasar Ruwanda a yayin da gudan ya dawo daga Dubai, duk mutanen biyu 'yan asalin kasar ne inji sanarwar gwamnati.

A kasar Yuganda kuwa, 'yan sanda sun kame tare da tsare wasu masu mu'amala ta jinsi daya, bisa zarginsu da yi wa dokar kasa ta hana yaduwar cutar Coronavirus karan tsaye. An kama gwanman 'yan luwadi da wasu 'yan daudu biyu a wani dan karamin gida da suke shakatawa, duk kuwa da dokar kasar na hana taron da ya zarta mutum goma da sa tazara a tsakanin juna. Kakakin 'yan sandan jihar da lamarin ya auku, Patrick Onyango, ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu, bisa take dokar kasa da yin sakacin da ka iya janyo yaduwar cutar ta Coronavirus a cikin kasar.

Yawan mutanen da suka kamu da cutar Coronavirus a birnin New York na kasar Amirka ya karu, inda yanzu ake da majinyata sama da dubu saba'in da biyar yayin da wasu fiye da dubu daya suka mutu, wannan na nufin an sami karin kashi ashirin da bakwai cikin dari na mamata inji Gwamnan jihar Andrew Cuomo. Kasar ta kasance tafka asarar rayuka fiye da kasar Chaina inda cutar ta samo asali.

A kasar Italiya, mutum akalla dari takwas da talatin da bakwai ne suka mutu a wannan rana ta Talata, sai dai gwamnatin kasar ta ce an yi nasara a fannin hana yaduwarta, ganin babu sabbin alkaluma na wadanda suka kamu da cutar. A Girka kuwa, mutum dari da biyu ne suka kamu da cutar kamar yadda bincike ya nunar. Daga ciki akwai wata mata 'yar gudun hijira da bata jima da haihuwa ba.

Kawo yanzu biliyoyin jama'a da ke karkashin dokar hana fita da jami'an kiwon lafiya da ke aiki ba dare ba rana a sassan duniya, sun kasa kunne don jin labarin samun magani koma riga-kafin cutar, da yanzu ta yi sanadiyar rayukan mutum sama da dubu talatin da biyar a sassan duniya.