1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar coronavirus ta bulla a Austria

Abdullahi Tanko Bala
February 25, 2020

A kasar Italiya kwayar cutar coronavirus ta yadu zuwa yankin Tuscany da tsibirin Sicily a cewar hukumar kare yaduwar cutattuka ta kasar yayin da a daya bangaren kuma aka sami bullar cutar a kasar Austria.

https://p.dw.com/p/3YOaP
Italien Mailand Coronavirus
Hoto: picture-alliance/dpa/D. Mascolo

Kasar Italiya dai ita ce kasar da ta fi yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a nahiyar Turai inda aka sami mutane 260 da suka kamu da kwayar cutar yawancin su a arewacin Italiya yayin da mutum bakwai kuma suka rasu.

Wasu rahotanni daga kasar Austria ma na cewa an sami mutum biyu da suka kamu da cutar. A cewar gwamnan yankin Tyrol, daya daga cikin wadanda suka kamu da cutar yana da alaka da makwabciya kasar Italiya.

Gwamnan lardin na Tyrol Guenther Platter ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Austria APA cewa an kebe mutanen biyu da suka inda ake kula da lafiyar su.

A waje guda kuma hukumar tarayyar Turai ta shawarci ma'aikatanta kada su je arewacin yankin Lobardy na Italiya saboda fargabar cutar ta coronavirus. Ta umarci su zauna a gida na tsawon makonni biyu.