WHO: Coronavirus ta zama annoba ta duniya
March 11, 2020Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana Cutar Coronavirus a matsayin annoba ga duniya, shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce an shiga wani hali na tsaka mai wuya a sakamakon yadda cutar ke ci gaba da yaduwa tana lakume rayuka ba tare da an iya shawo kanta ba. Ghebreyesus ya baiyana barnar da cutar ta yi a wasu sassan duniya fiye da ta'asar da aka gani a a kasar Chaina inda ta samo asali, duk da haka ya ce akwai sauran dabaru na dakile cutar in har an hada karfi da karfe a shirin tsarin lafiyan kasashen duniya.
A karon farko an sami wani mutum guda dauke da kwayar cutar ta Covid-19 a kasar Ivory Coast da ke yankin Yammancin Afrika. Ma'aikatar lafiyar kasar ta ce mutumin mai shekaru arba'in da biyar da haihuwa ya dawo kasar bayan shafe watanni a kasar Italiya. Tuni aka killace sauran mutanen da suka yi mu'amala da shi, kawo yanzu cutar ta bulla a kasashen Afrika bakwai daga cikin kasashen duniya kimanin dari da goma da ta yadu.
A nan Jamus ma dai, an gano wani jigo na jam'iyyar adawa ta AFD dauke da kwayar cutar. A labari mai nasaba da cutar ta Covid-19 ma, a kasar Italiya kuwa, wasu fursunoni goma sha biyu ne suka mutu bayan wani rikici da ya barke a tsakaninsu jami'an gidan yarin, wannan ya biyo bayan karfafa matakan tsaro da hukumomi suka yi don hana yaduwar cutar ta Coronavirus. Fursunoni sun bijirewa umarnin hana iyalansu ziyara da rage mu'amala a tsakaninsu, lamarin da ya janyo hatsaniyar da ta kai ga asarar rayuka da jikkata mutane da dama, akwai wasu da ake ci gaba da farautarsu bayan da suka tsere daga gidan yarin.