1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nemi karfafa matakan dakile cutar Coronavirus

Ramatu Garba Baba MNA
February 10, 2020

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya ce iftala'in annobar Coronavirus somin tabi ne don haka a tashi tsaye don dakile cutar kafin ta haddasa barna fiye da wanda ake gani yanzu haka a kasar Chaina.

https://p.dw.com/p/3XWgF
Tedros Adhanom Ghebreyesus -Generaldirektor der Weltgesundheitsorganisation (WHO)
Hoto: picture-alliance/S. Di Nolfi

Shugaban Hukumar lafiya ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya baiyana sakon ne a shafinsa na twitter a game da fargaba barkewar annobar Coronavirus a wasu sassan duniya inda ya nemi gwamnatoci da su tashi tsaye don yakar cutar da yanzu haka ta lakume rayuka fiye da dari tara a Chaina inda aka soma gano cutar.

Ghebreyesus ya nemi a dauki matakin ne bayan da aka gano, wasu kasashen da aka samu bullar Coronavirus, 'yan kasar ba su shiga koma taba yin mu'amala da 'yan kasar Chaina ba, wanda ya ce alamu ne da ke baiyana munin annobar, don haka ya nemi a dauki matakan gaggawa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kwararru na hukumar lafiyan ke kai ziyara Chinan a wannan Litinin, a wani yunkuri na son ganin an gano bakin zaren don dakile cutar. Kasashen duniya na ci gaba da aikin kwashe jama'arsu daga Chainan ganin yadda ta ke ci gaba da yaduwa. Cutar dai ta bulla ne a birnin Wuhan a Chainan inda yanzu alkaluman masu dauke da ita ya kai dubu arba'in.