1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina: Tallafin COVID-19 ga Afirka

Martina Schwikowski USU/LMJ
April 28, 2020

Daukacin kasashen Afirka sun daura damarar yaki da Coronovirus, kuma kusan dukkan kasashen nahiyar suna samun tallafin yin hakan daga kasar Chaina.

https://p.dw.com/p/3bVtM
Ägypten | Coronavirus | Produktion von Mundschutzmasken
Chaina na kai tallafin yaki da Coronavirus kasashen AfirkaHoto: picture-alliance/dpa/Xinhua

A kasashe kamar su Habasha da Burkina Faso, likitocin kasar Chaina sun jima da fara aiki da bayar da shawarin yadda za a shawo kan cutar. Wakilan DW a nahiyar Afirka, sun yi ta aiko da rahotannin yadda ake jibge kayayyaki  kama takunkumin fuska da na'urorin taya numfashi da rigunan kariya ga likitoci da ke fagen daga.

Agajin kamfanoni da attajirai

Bayaga ita kanta gwamnatin Chainan, kamfanonin kasar ma sun yi ta aika tallafi a yankunan da suka fi karfi, haka zalika shi ma hamshakin mai kudin kasar Jack Ma da gidauniyarsa sun tura kayayyakin agaji zuwa kasashen duniya da dama da suka hadar da Najeriya da Ruwanda da Kamaru da ma wasu kasashe da dama.

Nigeria Abuja | Coronavirus | Jack Ma Hilfsgüter
Tallafin kungiyar Jack Ma ga NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

A cewar Stephen Chan kwararre kan siyasar kasashen duniya da Afirka, wannan taimakon da Chaina ke ba su, batu ne jin kai. Dama dai Chaina ba bakuwar kasa ce a Afirka ba, domin  tun shekaru masu yawa ta ke gunadar da ayyukan gine-gine, kuma wajen agaji kasar na hobbasa a Afirka. Don haka taimako a yaki da annobar Covid19, sai dai kawai ya kara karfafa hulda ke tsakaninta da Afirkan a cewar masana.

To sai dai a 'yan makwannin nan al'amura na neman sauyawa, inda aka samu rahotannin cin zafarin 'yan Afirka mazauna Chainan musamman jihar Guangzhou. Hakan dai ya sanya kungiyar Tarayyar Afirka yin tsokaci a kai.

Fatan yafe basussuka

Sai dai masana na cewa, baya ga taimko a yaki da COVID-19 din, Afirka na da wata bukata a wajen Chaina, musamman neman ta yafe musu basussuka sakamkon tabarbarewar tattalin arziki. A daidai lokacin da annobar ke ci gaba da yaduwa a Afirka, tabbas hakan zai kara bai wa Chaina damar karfafa huldarta a nahiyar, a matsayin wacce za ta taimaka a tsamo su daga cikin tashin hankalin da suke fuskanta.