Coronavirus: Halin da ake ciki a sassan duniya
March 31, 2020Kasar Saliyo da ke yankin yammancin Afrika ta sanar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar ta Coronavirus a kasar. Shugaban kasar Julius Maada Bio ya tabbatar ma manema labarai cewa, mutumin mai shekaru talatin da bakwai da haihuwa, ya shigo kasar ce daga kasar Faransa. Kasar da ta tafka asarar rayuka daga annobar cutar Ebola ta dade da daukar matakan riga-kafi daga cutar Coronavirus, inda tuni ta rufe kan iyakokinta da sauran matakai na cikin gida don hana yaduwar cutar.
A nan Jamus kuwa, a mako mai zuwa ake shirin aiwatar da dokar amfani da kyalen rufe baki da hanci a karin matakan hana yaduwar cutar numfashi ta Covid-19. Ana sa ran aiwatar da dokar a yankin Thuringa da ke a gabashin Jamus, bisa shawarwari daga jami'an kiwon lafiya da ke ganin hakan zai taimaka wajen kare daidaiku da ya zame musu dole su fita aiki duk da dokar hana fita da gwamnatin kasar ta aiwatar.
An shawarci jama'a da su yi amfani da kowanne irin kyale a duk lokacin da za su fita.Alkaluma na jiya Litinin na nuni da cewa, mutum fiye da dubu sittin da biyu Coranavirus ta kama a Jamus, dari biyar da sittin da shida sun riga mu gidan gaskiya.
Kasar Thailand ta zama kasa ta farko a duniya da ta aiwatar da dokar hana sayar da barasa a kokarinta na hana yaduwar cutar Coronavirus. Dokar za ta soma aiki daga wannan rana ta Talata har zuwa sha shida ga wata mai kamawa. Dokar ta fi karfi a yankin Sakon Nakon inda duk wanda aka samu da laifin karya dokar, zai fuskanci hukuncin zaman gidan yari na shekara guda ko tarara kudi.Tuni kasar ta ayyana dokar ta bacci bisa annobar da ta karadde duniya.
Kawo yanzu dai babu tabbaci ko shan giya dama wasu barasa ka iya asassa cutar ta Coronavirus.