Za a iya samun karancin magunguna a nahiyar Turai
February 13, 2020Talla
A wani taro da ministocin kiwon lafiya na kasashen da ke cikin Kungiyar EU a birnin Brussels na kasar Beljiyam, ministan na lafiya na Jamus ya ce ya kyautu EU din ta nazari kan wannan batu don samo mafita cikin hanzari.
Ministan Spahn har wa yau ya ce akwai bukatar samun hadin kai da kuma fidda hanyoyi na tantance cutar tsakanin kasashen kungiyar don dakile yaduwar cutar.