Cotonou: Birni da ke bunkasa
Birnin Cotonou mai mutane dubu 800 shi ne birni mafi girma a Jamhuriyar Benin kuma cibiyar kasuwancin kasar. Tashar jirgin ruwan birnin na zama kashin bayan tattalin arzikin kasar, sai dai hakan na tattare da matsaloli.
Aikin gine-gine a birnin baki daya
Mutane na kara nuna sha'awar zama a Cotonou. Saboda haka ana bukatar muhimman tanade-tanade. A wani bangare na aikin gina sabbin hanyoyin mota, ana da burin gina sabbin tituna da sabunta wasu da kwaskware wasu da a jimilace tsawonsu ya kai kilomita 237 kafin karshen shekarar 2021 a birnin na Cotonou. Gwamnatin shugaban kasa Patrice Talon ta kaddamar da aikin.
Gagarumin aiki na kasaita: Marina
Sabon aikin gini na Marina. Titin da ke gefen gabar teku ya taso daga babban kantin Erevan da ke a gabar teku har zuwa layin Clozel, inda ake da manyan shaguna da yawa. Babbar hanya mai layuka shida, na da tsawon kilomita da yawa. Sai dai tun wasu shekaru ke nan ake aikin gina sabbin benaye a gefen titin Marina, amma har yanzu ba a kammala aikin gine-ginen ba.
An rusa rabin gidan amma babu diyya
An rusa wasu gidaje saboda aikin gina sabbin tituna, kamar yadda Ganfled da ke unguwar Fidjrosse ya shaida: an rusa wani bangare na gidanshi lokacin da aka zo aikin gina sabuwar hanyar da ta ratsa ta unguwar zuwa gabar teku. Yanzu ya rage masa dakuna biyu da bandaki guda daya. Ya yi korafi da cewa "ko da yake mun yi zanga-zangar adawa da rusaun, amma kawo yanzu ba a ba mu diyya ba".
Burin samun na kai
Ba hukuma ce kadai ke ba da kwangilar gini ba. Ana aikin sabbin gine-gine kusan ko-ina a unguwar Fidjrosse. Sabanin da, yanzu gidajen haya ne ga iyalai da dama ko kuma gidajen kasaita da sau tari masu bene hawa biyu zuwa uku ne. Yanzu da wahala a samu fili ko fuloti da babu gini a kai. Idan an samu to farashinsa ya ninka har sau uku idan aka kwatanta da lokutan baya, inji dillalai.
Babu fili ga kananan gidaje
Saboda haka dole ake rusa kananan gidaje da bukkoki. Ana aikin ginin har zuwa daidai iyaka da fulotin da ke makwabtaka. Sakamakon haka, sau da yawa, sabbin gine-ginen na rufe juna. Abin da ke bakantawa mazauna rai. Wannan shi ne nakasu ga bunkasar da birnin ke samu.
Saboda birni ya yi tsabta
Shara na karuwa daidai lokacin da al'umma ke bunkasa. Saboda haka a 2018 an kirkiro ma'aikatar kula da shara da sarrafa ta wato SGDS-GN. Baya ga kwashe shara da yanzu ake yi kyauta, kamfanin ne kuma ke kula da tsabtar gari da kuma kwalbatoci. Tun wasu makonni ke nan ma'aikata ke aiki tukuru a fadin birnin. Wannan gagarumin aiki ne.
Tsarin gina bayani? Ina!!!
Duk da wadannan matakan, Sènan Abraham Avakoudjo, da ke zama babban sakataren kungiyar masu zane da tsara birane a Benin, ya ce bai ga wani tsari mai dorewa ga birnin Cotonou ba. "Idan ana son a ci gaba da hadawa da tsarin gurguzu, dole a yi tunanin yadda duniya take yanzu." Bai dace a daga darajar wasu daidaikun ungwanni ba. Bai kamata a kori talakawa daga birnin ba.
Mutum 50 a tsakar gida guda daya
Mutane da yawa masu karamin karfi na rayuwa cikin kunci a Xwlacoji, wata unguwar masunta da ke tsakanin Tekun Atlantika da Kogin Nokoué. Daya daga cikin mazauna unguwar ita ce Martine Avinou, mai sana'ar sayar da soyayyar doya. Iyalinta na zaune a kananan dakuna biyu babu bandaki a ciki. A wasu lokutan mutum kusan 50 ke kwana a gidan mai dakuna biyar.
Rashin tsari na sufurin motoci
Duk da mummunan yanayi na gidajen zama, da yawa daga cikin mazauna Cotonou ba sa tunanin barin tsakiyar birnin. A Cotonou babu wani tsayayyen tsarin sufurin motocin safa-safa, in ban da "Benin Taxi". Da wayar tarho ake kiran tasi din masu launin dorawa da ke tsayawa a wurare da dama a birnin. Kudin daukar tasin ya yi kwatankwacin Euro 1.50
Birni na masu baburan Zéms
Mafi akasarin al'ummar birnin sun dogara da Zémidjans. Zéms, kamar yadda ake kiransu, babura ne da ake kabu-kabu da su. Sau da yawa dai sun fi sauri wajen sufurin mutane. Ga misali a kewayen kasuwar Dantokpa, mafi girma a kasar baki daya. Sai dai direbobinsu na yawan samun munanan haddura.
Take na kara gurgusowa
Birnin Cotonou na da wata matsala kuma: Birnin ba zai iya sake fadada a murabba'i ba. A arewacinsa akwai Kogin Nokoué, a kudancinsa Tekun Atlantika da ke kara zuwa kusa da unguwar Akpakpa. A tsohuwar unguwar "Zone des Ambassades" tuni gidaje da yawa suka kau, wasu kuma ba a iya zama cikinsu. Ana fata wata katangar dutwatsu a gabar teku za ta ba da kariya daga ambaliyar ruwan tekun.