Ghana ta yafe kudin lantarki ga jama'a
April 10, 2020Gwamnatin Ghana ta sanar da tsawaita dokar kulle da mako daya a biranen Accra da Kumasi. Wannan na zuwa ne a daidai loakcin da wa'adin zaman gidan na tsawon makonni biyu da ta dauka a a matakin hana yaduwar annobar Covid 19 ke shirin kawo karshe. A wani jawabi da ya gabatar a gidan talabijin na gwamnatin kasar a daren jiya Alhamis Shugaban kasar ta Ghana Nana Akufo-Addo yace matakin zai soma aiki daga ranar Litinin mai zuwa
Kazalika shugaban kasar ta Ghana ya kuma sanar da dauke wa 'yan kasar masu karamin karfi kudin wutar lantarkin watanni uku. Sauran 'yan kasar masu galihu da kamfanoni suma an dauke masu kaso 50 cikin dari na kudin wutar a tsawon watanni uku. Ya zuwa wannan Juma'a dai mutane 378 suka harbi da cutar Corona a kasar ta Ghana daga ciki shida cutar ta yi ajalinsu.