1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Coronavirus: Gwamnatin Najeriya ta tsawaita dokar hana fita

Ramatu Garba Baba
April 13, 2020

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, za a tsawaita dokar hana fita a wasu daga cikin jihohin kasar a kokarin da ake yi na ganin an hana yaduwar annobar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3aqtt
Muhammadu Buhari Nigeria
Hoto: picture alliance/AP Photo/S.Alamba

A wannan Litinin Shugaban Najeriyan ya yi wa 'yan kasar jawabi a game da yakin da kasar keyi da cutar Coronavirus, da yanzu haka ke ci gaba da yaduwa a kasar, ya tabo batun ragewa talakawa radaddin kuncin da suke ciki a sakamakon hana zirga-zirga don neman abinci, ya ce ana kokarin ganin kowa ya sami tallafin da gwamnati ta tanadar. Shugaba Buhari ya ce, za a tsawaita dokar hana fita a jihohin Legas da Ogun da kuma Abuja babban birnin kasar da karin makonni biyu.

Hukumar Lafiya ta Duniya(WHO) ta shawarci gwamnatoci da suyi taka tsantsana wajen sassauta matakan da suke dauka na hana yaduwar cutar Coronavirus. Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, akwai bukatar a kara matsa kaimi a fannin yin gwajin cutar da kuma kebe majinyatan da bincike ya tabbatar suna dauke da cutar. Mista Adhanom ya kara jan hankula a game da annobar da ya ce na tattare da hadura fiye da duk wata annoba da duniya ta fuskanta a can baya.

A Koriya ta Kudu, hannun agogo ne ya koma baya, bayan da aka gano wasu da suka warke daga cutar ta Coronavirus na dauke da kwayoyin cutar ta Covid-19. Lamarin ya zo ma Jami'an kiwon lafiya da mamaki inda tuni suka soma wani sabon bincike kan gwanman da aka gano suna da dauke da cutar a karo na biyu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin kasashen duniya, da suka ayyana tsauraran matakan yakar cutar, suka soma baiyana anniyarsu ta sassauta matakan da aka aza na hana yaduwar cutar da suka hada da dage dokar hana fita ya zuwa bude wasu kananan kamfanoni.