1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar dokar zaman gida a Afirka

Daniel Pelz ZMA/LMJ
April 27, 2020

An kafa dokar hana fita da nufin kare yaduwar cutar Coronavirus a nahiyar Afirka, sai dai dai mafi yawa daga cikin al'umma na cikin mawucin hali sakamakon yunwa da fatara da kuma tashe tashen hankula.

https://p.dw.com/p/3bTRw
Südafrika Lockdown Ausgangssperre
Jami'an tsaro na cin karensu babu babbakaHoto: AFP/M. Longari

Tun bayan da gwamnatin Kenya ta ayyana dokar hana fita a wani mataki na shawo kan matsalar yaduwar cutar COVID-19, kasar ta tsunduma cikin rikici, inda jami'an 'yan sanda suka soma cin karensu babu babbaka ta hanyar dukan mutane babu gaira babu dalili. Haka ma lamarin yake a Zambiya da Afirka ta kudu, a cewar kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa Amnesty International.

Tsaka mai wauya ga talaka

Alex Broadbent  farfesa ne a jami'ar Johannesburgh da ke nazarin cututtuka masu yaduwa, a cewarsa gallazawa mutane da 'yan sandan ke yi bai dace ba, inda ya ce a ra'ayinsa dokar hana fita ba ta da wani tasiri a Afirka, kuma hakan na nufin kulle mutane a gida tare da kassara kusan dukkan harkokinsu na tattalin arziki domin matakin bai dace da kasashe matalauta ba. Dokar hana fitar dai, ta jefa rayuwar miliyoyi masu ayyukan dogaro da kai cikin mawuyacin hali. Kashi 85 cikin 100 na 'yan Afirka, na cikin wannan rukuni. Kama daga masu aikin hannu da sayar da kaya akan tituna da kuma leburori.

China Entwicklungshilfe in Afrika Nigeria
Masu kananan sana'o'i na ji a jikaHoto: AP

Linda Chinenyeda ke cibiy ar nazarin harkokin rayuwar dan Adam a birnin Hamburg na nan Jamus, ta ce ba abun mamaki ba ne idan mutane sun ki bin dokar a afirka: "A nahiyar da kusan za a ce babu tsari na kyautata rayuwar al'umma ga marasa aikin yi. Idan har COVID-19 ba ta kashesu ba, to yunwa za ta kashe mutane. Dalili kenan da ya sa mutane ba sa iya kulawa da dokokin da aka gindaya musu, su na fita waje domin neman abinci".

Hasashen Majalisar Dinkin Duniya a kan Afirka na nuni da cewar, za a iya samun karuwar mutane miliyan 30 da za su kasance cikin fatara sakamakon annobar COVID-19.

Rana zafi inuwa kuna

Kungiyoyin agaji na gargadin cewar akwai yiwuwar mutane miliyan 50 a yankin Sahel na Afirka da ke fama da talauci, su fuskanci matsananciyar yunwa. Tuni dai birnin Lagos cibiyar kasuwancin Najeriya ya fara fuskantar wannan radadi.

Nigeria Lagos Stadtansicht
Lagos: Cibiyar cinikayyar NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa/A. Jallanzo

Abin fargabar a yanzu shi ne kar Afirka ta kasance wani wuri da wannan annoba za ta fi ta'azzar, ganin cewar tuni nahiyar ta tabbatar da mutane dubu 25 da suka kamu. Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen za a samu mace-mace na kimanin mutane dubu 300 cikin watanni masu zuwa. 

Barin jaki a bugi taiki

Farfesa Alex Broadbent na da ra'ayin cewar, rufe kan iyakokin yankuna zai taimaka maimakon garkame mutane a gida. "Abin da za a iya yi shi ne, hana zirga-zirgar tsakanin kasashe. Ba zaka ka hana jigilar kaya ba, sai dai ta mutane. Sai ka duba yankin da ke da cunkoson jama'a, ka kafa dokar hana shiga ko fita a yankin. Amma za a iya ci gaba da gudanar da harkokin kasuwanci a tsakanin mazauna yankin". 

Baya ga daukar matakan dai, nahiyar Afirka na bukatar mafita ta kanta, kuma an samu ci-gaba wannan fannin, kasancewar bincike ya yi nisa a Senegal kan gwajin maganin COVID-19 kana jami'ar Ghana na yin magungunan kashe cututtuka masu saukin farashi. Sai dai hakan ba ya nufin miliyoyin 'yan Afirka ba sa bukatar tallafin abinci.