1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta sassauta dokar zaman gida

Uwais Abubakar Idris LMJ
May 4, 2020

An fara aiki da sausauta dokar hana fita da aka sanya domin dakile yaduwar Coronavirus a Najeriya, bayan da gwamnati ta sanar da sassaucin a jihohin Lagos da Ogun da kuma Abuja babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/3blkg
Nigeria - Lagos | Abuja
Sassauta dokar zaman gida a biranen Abuja da Lagos da Ogun, ya haifar da cunkoso

Duk da sassauta dokar dai, an sanya ka'i'doji ga jama'a domin kaucewa yaduwar cutar ta COVID-19, musamman cikin motocin haya. Dimbin jama'a ne dai suka yi cincirundo suna jiran shiga mota a daya daga cikin unguwanin da ke Abuja, abin da ke nuna dawowar zirga-zirgar da da harkokin kasuwancin a birnin, abin da ya haifar da cunkoson motoci.

To sai dai, a daidai lokacin da ake murna da samun sasaucin inda dubban mutane suka fito don neman abincinsu, kwararru a fanin lafiya da suka hada da kungiyar ma'aikatan lafiya ta Najeriyar, suna nuna tsoron cewa bai kamata a sassauta dokar yanzu ba. Dr Ibrahim Kana kwararren likita a ma'aikatar lafiya ta Najeriya da ke kan gaba a yaki da yaduwar cutar, ya bayyana cewa akwai abin da ya kamata a yi la'akari da shi.

Tuni dai aka rufe kofofi na shiga jihohin Najeriya tare da daukar matakai na hukunta duk wanda ya sabawa dokar musamman sanya takunkumin rufe fuska da kuma kaucewa cunkoso. Abin jira a ganin shi ne yadda za a ci gaba da aiwatar da wannan sassauci, na tsawon makonni shidadomin kaucewa matsin tattalin arziki.