Coronavirus ta halaka mutun biyu a Afirka ta Kudu
March 27, 2020Ministan kiwon lafiyar kasar Zweli Mkhize ya tabbatar da labarin mutuwar mutanen biyu da cutar Cpovid-19 a lardin Cap na Kudu maso yammacin kasar, wanda hakan shi ne karo na farko da cutar ta yi kisa a kasar. Afirka ta Kudu tda ke da karfin masana'antu da kamfanonin na a matsayin kasar farko a kasashen Afirka da suk fara kamuwa da cutar ta coronavirus.
Shugaba Cyril Ramaphosa ya bukaci 'yan kasar miliyan 57 da su zauna a gidajensu har tsawon makonni uku, a wani mataki na dakile yaduwar cutar mai saurin yaduwa, kana kuma za a yi amfani da sojoji da sauran jami'an tsaro wajen tabbatar da doka da oda ta dakatar da mutane a gidajensu.
Sauran kasashen Afirka ma yanzu na fama da yaduwar cutar inda aka kiyasta sun kai mutun dubu biyu da 700 da suka harbu wasu akalla 73 suka mutu da annobar ta covid-19.